An kafa wani sabon kawancen adawa a Nijar

Shugaba Muhammadu Issofou da Shugaban Faransa
Image caption An kafa sabon kawancen adawa a Nijer, wata karin baraka a manyan jam'iyyun adawa na kasar.

A jamhuriyar Nijar an kafa wani sabon kawancen jam'iyyun adawa da ya kunshi tsohon kawancen ARN da jam'iyyar Moden Lumana ta shugaban majalisar dokokin kasar Malam Hama Amadu.

Kafa sabon kawancen mai sunan Ah-eR-De-eR ya biyo bayan ficewar jam'iyyar Moden Lumana daga kawancen da ke mulki na MRN a watan Agustan da ya gabata .

Wannan dai karuwar baraka ce a manyan jam'iyyun adawar kasar, inda har aka samu wasu bangarorinsu dake nuna goyon baya ga Shugaban kasa, har ma wasu suka karbi mukamai a cikin gwamnatin.

Karin bayani