An kashe mutane 5 suna Sallah a Damboa

Image caption Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau da mabiyansa

Rundunar sojin Najeriya ta ce 'yan Boko Haram sun kashe mutane biyar a wani hari da suka kai a wani masallaci dake garin Damboa na jihar Borno.

Sanarwar rundunar sojin wacce Kyaftin Aliyu Ibrahim Danja ya sanyawa hannu, ta ce an kai harin lokacin mutanen na Sallar subahi a ranar Asabar.

Amma kuma a cewar sojin, sun kaiwa jama'a dauki a garin, inda suka kashe mutane 15 daga cikin 'yan Boko Haram din.

Rahotanni sun nuna cewar rikicin 'yan Boko Haram ya janyo rasuwar mutane akalla 3,600 tun daga shekara ta 2009.

Sannan kuma 'yan Boko Haram suna kadammar da hare-hare a kan masallatai, da majami'u da makarantu da kuma gine-ginen gwamnati.

Karin bayani