Brazil ta gargadi Amurka da kawayenta

Shugabar Brazil Dilma Roussef
Image caption Rahotannin baya sun nuna Amurka na satar sadarwar shugabar Brazil Dilma Rousseff

Gwamnatin Brazil ta gayyaci jakadan Canada domin ba ta bayani kan zargin satar bayanai na baya bayan nan da tsohon jami'in leken asirin nan na Amurka, Edward Snowden ya tsegunta.

Wani rahoto da aka yada ta wani gidan talabijin na Brazil ranar Lahadi ya ce, jami'an leken asirin Canada sun rika satar gani da sauraron sadarwar ma'aikatar makamashi da ma'adanai ta Brazil.

A sakamakon yada rahoton shugabar Brazil Dilma Rousseff ta gargadi Amurka da kawayenta a shafin sadarwa na intanet na twitter cewa dole ne su dakatar da satar ganin bayanan da suke yi ba tare da wani jinkiri ba.