Masar: An kai hari a wurare uku

A Masar an kai harin bam a wurare uku da suka hada da wata hedkwatar jami'an tsaro, da kuma wani harin a kan wasu sojojin da ke sintiri.

Hakan na faruwa kwana daya bayan mutane fiye da hamsin sun hallaka a birnin Alkahira, a lokacin artabu tsakanin jami'an tsaro da magoya bayan Mohammed Morsi, shugaban kasar da aka hambarar, mai ra'ayin Musulunci.

Rabin ginin ofishin ya fadi kuma an ce mutane da dama sun makale a kasan baraguzan ginin.

Tashin bam din yazo jim kadan bayan kashe wasu sojojin Masar din su shida a kusa da birnin Ismailiya dake mashigar Suez.

Magoya bayan Muhammed Morsin sun sha alwashin ci gaba da fafatawa da dakarun tsaron kasar.

Karin bayani