PDP: Jonathan ya kara ganawa da gwamnoni

Image caption Batun zaben 2015 ne ya raba kan 'yan PDP

Shugaban Najeriya, Dr Goodluck Jonathan ya sake ganawa da wakilan gwamnoni bakwai da suka balle suka kafa sabuwar PDP ba tare da cimma wata yarjejeniya ba.

Yanzu dai sun dakatar da duk wata tattaunawa sai bayan an kammala aikin hajji.

Hudu daga cikin gwamnoni bakwai din da suka balle ne suka halarci gana wa da shugaban kasar, wadanda suka hada da na jihohin Kwara da Rivers da Kano da kuma Niger, kasancewar sauran takwarorinsu, wato da Gwamnan Jigawa da Sokoto da kuma Adamawa sun tafi Saudiyya sauke farali.

Baya ga shugaba Jonathan, shugaban kwamitin amintattun jam'iyyar PDP Mr Tony Anenih da wasu gwamnoni da ke jibintar jam'iyyar ta bangaren Bamanga Tukur su ma sun halarci zaman, ciki har da gwamnan jihar Kogi da na Akwa Ibom, da kuma jihar Katsina .

'Taro mara tsawo'

Ba kamar yadda suka saba da kwashe sa'o'i masu yawa suna ganawa a baya ba, a wannan karon tataunawar ba ta wuce sa'a daya da rabi ba.

Sai dai ita ma a sirri aka yi.

Kuma kamar yadda aka saba da zille wa mafi yawan 'yan jarida dake fadar shugaban kasar bayan irin wadannan taruka, haka aka zabi wasu 'yan jaridar kalilan da ba su wuce uku daga cikin sama da 'yan jarida saba'in da ke fadar ba bayan kammala taron na yau aka yi musu bayani a tsatsaye.

Gwamnan jihar Niger, Babangida Aliyu, shi ne ya karanta sanarwa bayan taron, wanda ya ce dukkan bangarori biyun sun amince za su ci gaba da duba hanyoyin sansantawa da juna.

Wannan matsayi za a iya cewa ba shi da maraba da wanda suka cimma a baya.

Karin bayani