Nijar ce ta karshe a amfani da intanet

Image caption Nijar ce kurar baya a cikin kasashen da ke amfani da intanet.

Wani bincike da Majalisar Dinkin Duniya ta yi ya nuna cewa Jamhuriyar Nijar da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ne kasashen da ke karshe a jadawalin kasashen da ke amfani da hanyar sadarwa ta intanet.

Binciken ya nuna cewa kasar Korea ta arewa ce kan gaba a kasashen da ke amfani da intanet a duniya.

A cewar binciken, Birtaniya ce ta takwas a jerin kasashe goma da suka fi amfani da intanet, inda ta wuce gaban Hong Kong da Japan.

Wani hasashe da jami'ai suka yi ya bayyana cewa kusan kashi 40 na mutanen duniya za su rika amfani da intanet a karshen shekarar da muke ciki.

Matsin lamba ga kasashe

Sai dai sun yi gargadin cewa tsadar intanet a kasashe masu tasowa tana yin tarnaki ga kasashen wajen bunkasa hanyar sadawar intanet.

Sun kara da cewa kashi 90 cikin 100 na mutane fiye da biliyan daya da ba sa amfani da intanet suna zaune ne a kasashe masu tasowa.

Binciken ya zayyana kasashe 39 da ba sa amfani da intanet yadda ya kamata, kuma akasarinsu a nahiyar Afirka suke.

A karshe, binciken ya ambato wata gamayyar kungiyoyin da ke samar da intanet mai suna The Alliance for Affordable Internet a turance, tana bayyana aniyarta ta matsawa kasashe lamba domin su samar da hanyoyi masu rahusa na samun intanet.

Karin bayani