Jonathan ya kaddamar da kwamitin taron kasa

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan
Image caption An baiwa kwamitin makonni shida ya kammala aikinsa

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya kaddamar da kwamitin da zai tsara yadda za a gudanar da babban taro na kasa.

Kusan mako gudana kenan da shugaban ya bada sanarwar shirya taron, da zummar magance matsalolin da suka dabaibaye kasar da kuma tantance makomarta.

Wasu 'yan Najeriyar na ganin taron zai yi tasiri mai kyau, yayin da wasu kuma ke da ra'ayin cewa, ba shi da wani amfani.

Rahotanni na cewa daya daga cikin mambobin kwamitin, farfesa George Obiozor ya nemi a cire shi daga kwamitin, saboda dalilai na rashin lafiya.