Saudi: Za'a yi wa malami bulala 600

Image caption Abdallah, Sarkin Saudiyya

An yankewa wani malami mai wa'azi a kasar Saudia hukuncin daurin shekaru takwas a gidan kaso tare da bulala dari shida, saboda laifin azabtarwa da dukan 'yar sa mai shekaru biyar da ya yi sanadiyyar mutuwar ta.

A farkon wannan shekarar ne labarin Fayhan Al Ghamdi ya bayyana inda ya ja hankalin jaridu a kasashen duniya kan cewa mai yuwa kotu ta wanke shi.

Hakan ta sa masu fafutuka suka fara gamgami da sunan yarinyar Lama, domin matsa lamba kan mahukuntan Saudiyya.

Akan nuna Al Ghamdi a tashoshin talbajin na tauraran dan adam a Saudiyya yana wa'azi, ko da ya ke a hukumance ba'a daukar sa a matsayin malami.