Amurka ta yaba wa Syria

John Kerry da Sergei Lavrov
Image caption Kerry ya ce Syria tana ba da hadin kai ba wata kumbiya-kumbiya

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya ce gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad ta cancanci yabo kan yadda take ba da hadin kai ga shirin Majalisar Dinkin Duniya na lalata makamanta masu guba.

Da yake magana yana tare da takwaransa na Rasha Sergey Lavrov a wurin taron shugabannin kungiyar kasashen Asia da Pacific a Indonesia, Mr Kerry ya ce Amurka da Rasha na yabawa da ci gaban da ake samu.

Kwararrun jami'ai masu lalata makaman masu guba sun isa birnin Damascus ne kasa da mako daya kenan.

A cewar Jami'an Majalisar Dinkin Duniya, ma'aikatan na Syria ne suka gabatar da na'urorin da aka yi amfani da su wajen lalata wasu abubuwan da dama.

Wadannan abubuwan kuma sun hada da makaman masu linzami da bama-baman ragargaza wasu wurare da na'urar cakuda gubar da dura ta._

Karin bayani