Mummunar zanga-zanga a Brazil

Zanga zanga a Brazil
Image caption Zanga zangar malaman makaranta a Brazil ta kare da rikici a titunan biranen Rio de Janeiro da Sao Paulo.

Zanga-zangar malaman makaranta a Brazil ta juye zuwa tashin hankali a titunan biranen Rio de Janeiro da Sao Paulo.

Masu zanga-zanga sama da dubu goma ne suka yi tattaki a tsakiyar birnin Rio cikin lumana, to amma da duhu ya fara yi sai kawai wani gungun matasa da suka rufe fuskokinsu suka shiga kokarin fasa gidaje da sauran wurare.

Matasan sun yi kaca-kaca da wani ofishi na bankin Brazil, inda suka dauki na'urorin ba da kudi.

A can Sao Pualo ma zanga-zangar da aka yi ta marawa malaman da suka shirya ta Rio baya, ta kare da dauki ba dadi da 'yan sanda.

Karin bayani