Mutane 30 sun mutu a Afirka ta Tsakiya

Pira Ministan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Nicolas Tiangaye
Image caption Pira Ministan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Nicolas Tiangaye

Mutane talatin suka rasu , da dama suka jikkatai a jamhuriyar Afrika ta tsakiya, bayan barkewar rikici a arewa maso yammacin kasar.

Rikicin ya barke ne tsakanin tsoffin masu tada kayar baya na hadaddiyar kungiyar Seleka da kuma tawagar wasu 'yan banga.

Rahotanni sun ce, masu tayar da kayar bayan sun kai hari ne wani kauye mai suna Garga, a ranar Litinin din da ta gabata daga nan ne kuma fada ya rincabe inda aka cigaba da gwabzawa a ranar Talata.

Jamhuriyar Afrika ta tsakiya ta fada rikici ne tun bayan lokacin da masu tada kayar baya suka hambarar da gwamnatin shugaba Francois Bozize a watan Maris.