Samar da intanet mai araha a Najeriya

Internet mai rahusa ga talakka
Image caption Wasu kamfanoni sun fara yunkurin samar da intanet mai rahusa ga talakawa a kasashe masu tasowa

Wata gamayyar kamfanonin sadarwa na gwamnati da masu zaman kansu na kasashen duniya sun kaddamar da wani shiri na samar da hanyar sadarwar intanet mai arha ga al'ummomin kasashe masu tasowa.

Gamayyar mai suna kawancen A4 AI na son kawo sauye-sauye ne domin taimakawa wajen ganin kudin da ake chajin mutane wajen amfani da intanet ya ragu zuwa kashi biyar cikin dari na kudaden shiga mafi karanci da talaka ke samu a wata.

Wanda shi ne burin da hukumar kula da sadarwar intanet ta Majalisar Dinkin Duniya ke fatan ganin an cimma.

A yanzu ne kasashe kamar Najeriya, ke yunkurin samar da hanyar intanet mai saurin gaske wato Broadband, domin wajen habaka tattalin arzikinta, ko da yake wasu na hasashen karancin wutar lantarki ka iya yin kafar ungulu ga shirin.

Karin bayani