Masu fafutuka a Mali sun rusa gadar Gao

Dakarun soji a Gao

Wasu da ake zargin masu fafutukar Islama ne a arewacin Mali, sun rusa gadar birnin Gao.

Hukumomi a kasar sun ce lamarin ya auku ne a babban titin dake zuwa bakin iyakar kasar da Nijar, harin da ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula biyu.

Bayan an shafe watanni a karon farko, a ranar litinin din da ta gabata ne, masu kishin Islamar suka kai hari na farko.

Masu fafutukar dai sun mamaye arewacin kasar na tsawon watanni, kafin dakaru karkashin jagoranci Faransa su fatattake su a farkon shekarar nan.