Ana son kafa tawagar ceto masu kaura

Masu aikin ceto a Lampedusa
Image caption Jirgin ruwan ya kama da wuta kafin ya nutse da 'yan gudun hijiran da mafi yawansu 'yan Afrika ne

Hukumar Tarayyar Turai ta bada shawarar kafa wata tawaga a tekun Mediterranean, domin kama jiragen ruwan dake dauke da 'yan gudun hijira.

Shawarar da kwamishiniyar cikin gida, Cecilia Malmstroem ta bayar na zuwa ne, bayan masu kaura 230 sun mutu a yayin da jirginsu ya nutse a kusa da tsibirin Lampedusa.

Za ta mika shawarar ga ministocin kungiyar a Luxembourg a ranar Talata.

Ana tsare da matukin jirgin wani dan Tunisia a Sicily, bisa zargin kisan kai ba da gangan ba.