Kotu ta yi watsi da tuhumar 'yan Rasha

Wani jirgin ruwan Rasha mai gadin bakin tekun kasar
Image caption Shari'ar ta kawo karshen dangantakar diplomasiyyar da ta fara rauni tsakanin Rasha da Najeriya

Wata babbar kotun tarayya da ke Lagos a Najeriya, ta yi watsi da tuhumar da ake wa wasu 'yan kasar Rasha, ma'aikatan jirgin ruwa su bakwai.

Mutanen na cikin ma'aikata jirgin ruwa 15 da ake zargi da shigar da makamai ba bisa ka'ida ba cikin Najeriyar.

Hukumomi a Najeriyar sun kama jirgin ruwan mallakar wani dan kasar a ranar 23 ga watan oktoba a bara, dauke da bindigogi da dubban albarussai.

Lauyan dake kare 'yan Rashan ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa, 'yan Najeriya biyu dake cikin jirgin ruwan su ne suka yaudari 'yan rashan da cewa sun samu izinin shiga kasar da makaman.