'Tattalin arzikin Palasdinawa zai bunkasa idan...'

Image caption Rahoton ya yi gargadin cewa tattalin arzikin Palasdinawa zai ci gaba da tabarbarewa

Babban bankin duniya ya ce tattalin arzikin Palasdinawa zai bunkasa da fiye da kaso 33 cikin 100 idan Israila ta janye daga mamayewar da ta yi wa yammacin kogin Jordan.

Wani sabon rahoto da Bankin ya fitar ya ce tattalin arzikin Palasdinawa zai ci gaba da tabarbarewa sakamakon kin ba su damar yin amfani da albarkatun kasarsu.

Israila dai ta ce za a tattauna a kan rahoton da Bankin duniyar ya fitar lokacin taron da za a yi tsakaninsu da Palasdinawa.

A karkashin yarjejeniyar Oslo, an raba ikon gabar yammacin kogin Jordan zuwa gida biyu --inda Isra'ila ke gudanar da albarkatun kasa yankin -- su kuma Palasdinawa ke gudanar da bangaren mulkin yankin.

Karin bayani