An shigar da Majalisar Dinkin Duniya kara

Wata mata mai fama da cutar kwalara a Haiti
Image caption Majalisar Dinkin Duniyar tace tana da kariya daga tuhuma

Lauyoyin dake kare wasu da cutar kwalara mafi muni a tarihi ta shafa a kasar Haiti, sun shigar da Majalisar Dinkin Duniya kara a New York a ranar Laraba, suna neman diyya na miliyoyin daloli.

Ana son Majalisar ta biya diyyar ne a madadin fiye da mutane dubu takwas da suka mutu, da kuma dubban daruruwa da suka kamu da kwalara a shekarar 2010.

Lauyoyin masu shigar da kara sun yi nuni da cewa, dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar ne suka kai cutar kasar.

Bincike ya nuna cewa an samu yoyon bahaya a sansanin dakarun Nepal dake fama da cutar, abin da ya janyo barkewar kwalara a Haiti.