Kamfanonin salula sun sha tambayoyi a Kenya

Shugabannin kamfanonin wayoyin salula na Kenya
Image caption Shugabannin kamfanonin hudu sun fuskanci tambayoyi daga jami'an 'yan sanda

Shugabannin kamfanonin wayoyin salula a Kenya, sun musanta zargin cewa sun sayar wa jama'a layukan wayoyin salulan da ba'a yi wa rajista ba.

Hakan ya biyo bayan rahotannin dake nuna cewa mutanen da suka kai hari kan rukunin shaguna na Westgate a Nairobi sun yi amfani da layukan da ba a yiwa rajista ba.

Gwamnati kasar ta yi barazanar kamasu, saboda sun bari an yi amfani da layukan wayoyin salular da ba'a yi wa rajista ba.

A shekarar 2010 ne Kenya ta maida da shi dole a yi rajistar dukkan layukan salula, domin rage aikata manyan laifuka da hare-haren masu tada kayar baya.