Masar ta tsayar da ranar shari'ar Morsi

Magoya bayan Mohamed Morsi
Image caption Daruruwan magoya bayan Morsi dakaru suka kashe, a lokacin da suka tarwatsa masu zaman durshen

Kasar Masar ta sanar da ranar 4 ga watan Nuwamba, a matsayin ranar da za a fara shari'ar hambararren shugaban kasar, Mohamed Morsi.

Ana tuhumar Mista Morsi tare da wasu 'ya'yan kungiyar 'yan uwa Musulmi da laifin ingiza mutane, domin kisan kai.

Tuhumar na da alaka da kisan wasu masu bore a wajen fadar shugaban kasa, a yayin zanga-zangar da aka yi a bara.

Tumbuke Morsi ya janyo bore daga magoya bayansa, kuma an kashe da dama daga cikinsu a artabu da jami'an tsaro.