Najeriya ta yi martani kan hari a Guinue

Image caption Shugaba Jonathan da wasu shugabannin Afirka

Gwamnatin Najeriya ta ce harin da aka kai kan ofishin jakandancinta da ke kasar Guinue Bissau ba zai sanyaya mata gwiwa ba game da rawar da takawa wajen tabbatar da mulkin dimokradiyya a Afirka.

Najeriyar ta ce a matsayinta na babbar yaya, hakki ne da ke wuyanta ta taimaka wajen wanzar da zaman lafiya da ci gaban kasashen da ke nahiyar.

A ranar Talata ne dai wasu suka kai hari kan ofishin jakadancin nata da ke kasar Guinea Bissau, inda a kalla mutum daya ya rasa ransa.

Wasu dai sun yi hasashen cewa harin zai iya sanyawa dangantaka ta yi tsami tsakanin kasashen biyu.

Karin bayani