Nissan zai fara hada motoci a Najeriya

Nissan

Kamfanin hadin guiwa na Renault da Nissan, ya kulla wata yarjejeniya sharar fage da kamfanin Stallion da ke Afrika ta Yamma, domin kafa kamfanin hada motoci a Najeriya.

A karkashin yarjejeniyar, kamfanin Stallion wanda dama yake dillancin motocin Nissan a Najeriya, zai bunkasa kamfaninsa da ke Lagos.

Dama dai kamfanin na Stallion a yanzu haka yana kera motocin haya a kamfaninsa da ke Lagos, to amma za'a kara yawan motocin da kamfanin ke kerawa a kowace shekara zuwa 45,000.

Kamfanin Nissan na kokarin mayar da Najeriya wata cibiya ta kera motoci a nahiyar Afrika.

Wannan mataki ya zo ne a yayin da gwamnatin Najeriya ke kokarin amincewa da wata sabuwar manufa da nufin karfafawa kamfanonon motoci a kasar gwiwa, domin rage yawan motocin da ake shiga da su kasar.