Fasinja ya saukar da jirgi bayan suman matukin

Image caption Fasinjan bai taba tuka jirgi ba

Wani fasinjan da bai taba tuka jirgi ba ya saukar da jirgin sama lafiya bayan da cutar ajali ta kama direbansa a sararin samaniya.

Wannan lamari ya auku ne a Ingila, inda fasinjan ya yi ta maza, ya kwace sitiyayin jirgin, kana ya sauke shi a filin jiragen sama na Humberside.

Malaman horar da matuka jirgin sama guda biyu ne suka rika bai wa fasinjan umarni ta wayar tarho kan yadda zai tuka jirgin bayan direban jirgin ya fita daga hayyacinsa.

Matukin jirgin da fasinjan su kadai ne a cikinsa.

Daya daga cikin malaman, Mista Murry, ya ce fasinjan ya sauko da jirgin kamar yadda kwararren direban jirgi ke yi.

'Yan sanda dai sun tabbatar da mutuwar matukin jirgin na asali, koda yake ba su kai ga gano abin da ya yi sanadiyar mutuwarsa ba.

Karin bayani