Masu fafitika a Masar sun gudanar da addu'oi

Birnin Alkahira na kasar Masar
Image caption Birnin Alkahira na kasar Masar

Daruruwan masu fafutuka a kasar Masar sun gudanar da addu'oi da kunna kyandir da daddare don tuna zagayowar mutuwar wasu kiristoci masu zanga-zanga.

An dai kashe su ne a wata taho mu gama da jami'an sojoji shekaru biyu da suka gabata.

Mutane ashirin da biyar ne aka kashe, a abinda suka kira kisan gillan Maspero.

Ya faru ne bayan da sojojin a motoci masu sulke suka farwa kiristocin da ke gudanar da zanga-zanga a wajen ginin gidan talbijin na kasar da ke dandalin Maspero.

Wasu daga cikin wadanda suka halarci wadannan addu'oi na rera taken da ke nuni da kin abinda sojojin suka aikata, yayin da wasu kuma suka ce sojojin sun kubutar da kiristocin daga harin kungiyar 'yan uwa musulmi.