Zanga-zanga kan karin kudin wuta a Ghana

Birnin Accra na kasar Ghana
Image caption Birnin Accra na kasar Ghana

A birnin Accra na kasar Ghana, wata kungiya mai zaman kanta da ake kira Truth and Accountability Forum, ta yi zanga-zangar nuna adawa da kara kudin wuta da ruwa.

Kungiyar ta ce karin ya yi yawa saboda haka jama'a ba za su iya biya ba.

An dai kara kudin wutar ne da kashi 78 cikin dari, na ruwa kuma da kashi 52 cikin dari.

A ranar daya ga watan Oktobar da muke ciki ne dai, sabbin farashin wutar da na ruwan da hukumomin kasar suka sanar ya fara aiki.