An sace Firayi ministan Libya

Firaministan Libya Ali Zeidan
Image caption Firaministan Libya Ali Zeidan

Shafin intanet na gwamnatin Libya ya ce wasu masu dauke da makamai sun yi awon gaba da Firaministan kasar Ali Zeidan.

Shafin ya ce an dauke shi ne da sanyi safiya daga wani Otel din da yake a Tripoli a bisa dalilin da ba a sani ba kawo yanzu.

Wakiliyar BBC a Tripoli ta ce ana zargin wasu jami'an 'yan sanda da ke da alaka da gwamnati da hannun wajen sace shi.

A makon da ya gabata ne dakaru na musamman a Amurka suka sace Abu Anas al-libi, wanda ake zargi shi ne kusa a kungiyar alka'ida.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba