Za a maida Charles Taylor Birtaniya

Image caption A bara ne wata kotu ta samu Charles Taylor da laifi

Birtaniya ta tabbatar da cewa za a dawo da tsohon shugaban kasar Liberiya, Charles Taylor kasarta domin yayi zaman sarka na shekaru hamsin da aka yanke masa kan aikata miyagun laifukkan kan bil'adama.

Ministan Shari'a na Birtaniya, Jeremy Wright ya ce sun amsa bukatar da kotun musamman kan shari'ar laifukkan yaki ta kasar Saliyo ne.

An samu Mr Taylor ne da laifin mara baya ga 'yan tawayen Saliyo a lokacin mummunan yakin basasar kasar a shekarun 1990.

Makonni biyu da suka wuce ne aka yi watsi da karar da Mr Taylor ya daukaka kan hukuncin da aka yanke masa.

Karin bayani