ICC ba ta adalci ga 'yan Afrika - Minista

Shalkwatar kungiyar tarayyar Afrika a Habasha
Image caption Kungiyar na zargin ICC da farautar 'yan Afrika

Kotun hukunta manyan laifukan yaki ta duniya ICC, ba ta yin adalci ga mutanen Afrika a cewar wani babban jami'i a yayin fara taron kungiyar tarayyar Afrika a Addis Ababa.

Ministan harkokin wajen Habasha, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce kotun da ke zamanta a Hegue ta zama ta siyasa, kuma bata adalci ga 'yan Afrika.

Taron na kwana biyu da aka fara a ranar Juma'a, zai tattauna batun dangantakar da ta soma tsami tsakanin kasashen da kotun ta ICC.

Kuma ya zo a ne a lokacin da shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta zai gurfana a gaban kotun a watan gobe.