Sabuwar PDP ta yi raddi ga INEC

Baraje da gwamnoni bakwai a lokacin da suka ziyarci majalisa
Image caption Baraje da gwamnoni bakwai a lokacin da suka ziyarci majalisa

Bangaren Jam'iyar PDP da ya balle a Najeriya, ya maida martani kan matsayin hukumar zaben kasar INEC, na tabbatar da Alhaji Bamanga Tukur a matsayin shugaban jam'iyyar.

Sakataren tsare-tsare na sabuwar PDP, Alhaji Nasiru Isa Abubakar ya ce matakin na INEC bai basu mamaki ba, saboda hukuma ce dake karkashin gwamnati.

Ya kuma kara da cewa za su daukaka kara game da hukuncin kotun tarayya ta Legos, wacce ta yi watsi da karar da suka shigar na kalubalantar Bamanga.

Sakataren tsare-tsaren ya ce za su cigaba da gwagwarmayar da suke yi, musamman ganin daga gwamnati har jam'iyyar babu wanda ya musanta korafe-korafensu.