Firaministan Libya ya bayyana wadan da su ka sace shi

Firaministan Libya Zeidan
Image caption Firaministan Libya Zeidan

Firaministan Libya, Ali Zeidan ya ce 'yan bindigar da suka sace shi a farkon makonan na daga cikin wadanda suka yi kokarin yi masa juyin mulkin wanda 'yan adawa da ke cikin majalisar dokoki suka shirya.

Mr. Zeidan ya yi wannan ikirarin ne a cikin wani jawabi da ya yiwa al'ummar kasar wanda aka watsa a gidan talbijin na kasar.

Bai dai bayyana suna yen wadanda suka sace shi ba, amma ya dora laifin akan wadanda ya kira marassa rinjaye a cikin majalisar dokokin kasar.

Wakiliyar BBC a Tripoli ta ce, wadannan kalaman na sa sun nuna irin barakar da ke akwai a cikin majalisar dokokin kasar.

Karin bayani

Labaran BBC