Ministar kudin Najeriya

Image caption Ngozi Okonjo-Iweala ta yi fice sosai a kan tattalin arziki

An haifi Ngozi Okonjo-Iweala ne a shekarar 1954.

Fitacciyar masaniyar harkokin tattalin arziki ce. Ta yi suna ne sosai bayan ta zama ministar ma'aikatar kudi sau biyu (har yanzu minista ce) a Najeriya.

Haka kuma ta shahara saboda aikin da ta yi a Babban Bankin Duniya, a matsayinta na manajar daraktar Bankin daga shekarar 2007 zuwa 2011.

Ta rike mukamin ministar harkokin kasashen wajen Najeriya na dan wani lokaci a shekarar 2006.

A shekarar 2007, an yi ta sa ran cewa ita ce za ta maye gurbin shugaban babban bankin duniya na wancan lokacin, Paul Wolfowitz.

A shekarar 2012, Ngozi tana daga cikin mutane uku da suka yi takarar shugabancin Babban Bankin Duniya domin maye gurbin Robert Zoellick

Sai dai shugaban bankin na yanzu, Jim Yong Kim, ya yi nasara.

Karin bayani