'Yan sanda mata a Kano

Image caption Daya daga cikin daruruwan mata 'yan sanda a Najeriya

A mafi yawan kasashen Africa, aikin dan sanda aiki ne da yawanci maza ne ke yinsa, amma a shekarun baya-bayan nan, ana samun karuwar matan da ke shiga aikin.

A jihar Kano dake arewacin Najeriya a yanzu ana samun mata masu aikin 'yan sanda.

To ko ya ya ake kallon mace 'yar sanda a al'ummar Hausa-fulani?

Kuma wane irin kalubale suke fuskanta a wajen aiki da kuma a cikin al'umma?

Sufetar 'yan sanda, Ramatu Muhammad wadda ta kwashe shekaru 22 tana aikin, ta yi bayanin abin da ya sa mata ke shiga aikin 'yan sanda.