Malta ta damu kan hadarin jirgin ruwa

Hadarin jirgin ruwan 'yan gudun hijira
Image caption Hadarin jirgin ruwan 'yan gudun hijira

Fira Ministan kasar Malta Joseph Muscat ya ce tekunan yanin Turai dake kusa da Afirka yanzu na neman zama wata makabarta.

Ya bayyana hakan ne saboda yawan abkuwar hadarin bayan da wani jirgin ruwa dauke da daruruwan 'yan ci rani ya sake nutsewa tsakanin tsibirin Sicily na kasar Italiya da kasar Tunisia.

Mutane 27 aka bayyana sun halaka yayin aka kubutar da kimanin dari biyu, bayan aikin ceton da masu gadin gabar teku na kasashen Italiya da Malta suka gudanar.

Mr Muscat ya ce abin kunya ke ga kasashen Turai, ganin irin yadda ake ta samun jerin abkuwar bala'oin da suka haddasa mutuwar daruruwan jama'a.

Ya kuma ce dole ne sai Kungiyar Tarayyar Turai ta nemi hanyoyin warware abkuwar matsalar na tsawon lokaci.