'Yansanda a Enugu sun bullo da wani shiri kan tsaro

'Yansandan Najeriya
Image caption 'Yansandan Najeriya

A Najeriya, rundunar 'yan sandan jihar Enugu ta bullo da wata sabuwar kafar sadarwa ta intanet, domin samun bayanai daga wajen jama'ar gari da sauran masu ruwa da tsaki a sha'anin tsaro.

Rundunar ta na ganin wannan hanya za ta kara taimakawa wajen kyautata dangantaka tsakaninta da sauran jama'a.

Ta ce hakan zai su rinka samar mata muhimman bayanan da suka kamata, wadanda za ta yi amfani da su wajen ci gaba da yaki da miyagun laifuffuka a jihar.

Sai dai kuma duk da haka, har yanzu jama'a su na da sauran shakku wajen sakin jiki da 'yan sandan.