Yau ake sanar da zakaran kyautar Mo Ibrahim

Mo Ibrahim
Image caption Mo Ibrahim

A yau ne za'a sanar da wanda ya lashe kyautar Mo Ibrahim ta kyakkyawan Shugabanci a Afrika.

A bara dai babu shugaban da ya lashe kyautar domin ba'a ga sun samu wata nasara ba ta fannonin tsaro da kiwon lafiya da ilmi da kuma ci-gaban tattalin arziki.

Za'a baiwa duk wanda ya lashe kyautar kudi daya kai dalar Amurka miliyan biyar nan take, sannan a rika ba shi dala dubu dari biyu a kowace shekara har karshen rayuwarsa.

Tun da aka fara ba da kyautar a shekara ta 2007 dai mutane uku ne suka samu nasarar lashe ta wadanda suka hada da shugaba Joachim Chissano na Mozambique, da Festus Morgae na Botswana da kuma Pedro Pires na Cape Verde.

Gidauniyar Mo Ibrahim ce dai ke ba da kyautar ga shugabannin kasashen Afrika wadanda suka ciri-tuta wajen samar da tsaro, da kiwon lafiya da Ilimi da kuma ci-gaban tattalin arziki a kasashensu; da kuma wadanda suka yi nasarar mika mulki ga wadanda suka gaje su ba da wata gardama ba.