India: Mutane 89 sun mutu a turmutsitsi

'Yan sanda a India sun ce akalla mutane tamanin da tara ne suka rasu yayin turmutsitsi a wajen wani bikin ibadar 'yan Hindu da ake yi shekara shekara.

Lamarin ya faru ne lokacin da dubban masu ibadar suke kokarin tsallaka wata 'yar ƙaramar gada zuwa wurin ibadar dake Madhya Pradesh.

'Yan sanda sun ce, lamarin ya faru ne yayin da ake yada jita-jitar cewa, gadar zata rufta.

Wasu mutanen an tattake su ne wasu kuma suka sun nutse ne a ruwa.