Italiya na kara sintiri a tekun Bahar Rum

Ma'aikatan ceto a Italiya
Image caption Ma'aikatan ceto a Italiya

Kasar Italiya tana kara yawan jami'an tsaronta da ke aikin sintiri a tekun Bahar Rum yayin da take fadada aikin nema da ceton 'yan ci rani daga kasashen Afrika a tekun.

Ana saran sojoji dake sintiri za su maida hankali a yankunan da suka hada da Sicily, da Malta da kuma gabar tekun Libya.

Wannan shiri da hukumomi a Italiya suka bullo dashi nada zummar ganin an kaucewa abkuwar hadurran jiragen ruwa ne a tekun a nan gaba.

Tun bayan da wani jirgin ruwa ya nutse da bakin haure 150 ne a tsibirin Lampedusa Prime ministan Italiya Enrico Letta ya yi ta fuskantar matsin lamba na ya inganta matakan samar da agaji.

Italiya da Malta na son sauran shugabannin kasashen Turai su ma su dauki irin wannan mataki a babban taron da za su yi a wata mai zuwa.