An rufe masaukin gwamnan Adamawa a Abuja

Gwamnan Jihar Adamawa Murtala Nyako

A Najeriya Hukumar Abuja babban birnin tarayyar kasar ta rufe masaukin gwamnan jihar Adamawa da ke birnin bisa zargin ana amfani da shi ta hanyar da ba ta dace ba.

Hukumar ta ce ana amfani da masaukin wajen yin tarukan siyasa. Sai dai gwamnatin jihar a nata bangaren ta yi zargin cewa an rufe ofishin ne saboda Gwamnan jihar da wasu takwarorinsa ba sa goyon bayan sake tsayawa takarar shugaba Jonathan a shekara ta 2015.

Alhaji Aminu Iyawa kwamishinan raya karkara kuma shugaban majalisar kwamishinonin Jihar Adamawa yace idan har babu siyasa a matakin da hukumar birnin tarayya Abuja ta dauka akan masaukin gwamnan Adamawa, to kamata ya yi hukuncin ya shafi sauran masaukan gwamnoni dake unguwar ta Asokoro.

Yace matakin ba zai raunana su sai ma ya kara musu karfin gwiwa.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba