Hana matan Ibo gado a Najeriya

Wasu mata a Najeriya
Image caption A wasu kauyuka za a iya barin mace ta yi noma a filayen mijinta da ya mutu, amma ba za ta gaje su ba

Ana hana akasarin matan al'ummar Ibo na kudu maso gabashin Najeriya, gadon kadarorin mazajensu da suka mutu, al'amarin da matan yankin ke kururuwan cewa yana tattare da wariya a gare su.

Domin ya kan jefa matan da kuma marayu cikin matsalar fatara da sauran wahalhalun rayuwa.

Sau tari kuma takaddamar al'adar hana mata gadon kadarori, a kan warware ta ne ta hanyar yarjejeniya tsakanin dattawa a gida ko wajen sarakunan gargajiya, ba a bari batun ya isa kotu.

Kungiyoyin kare hakkin mata na ikirari cewa, hakan ya keta hakkin mata na samun daidaito da kuma martaba, to ko shin akwai wani kokari da ake yi domin sauya wannan al'ada?

Dalili

Tsohuwar shugabar kungiyar 'yan jarida mata reshen jihar Enugu, Maureen Atuonwu mai fafutukar kare hakkin mata ta ce, ba a bari mata su sami gadon kadarorin mahaifinsu, saboda amannar cewa zai koma hannun mazajensu.

Haka kuma idan mijin mace ya mutu, kuma ba ta ta haifi da namiji ba, sai dangin mijinta su shiga kokowar mallakar kadarorinsa, saboda za su ce, idan 'yar ta yi aure, ba wanda zai dauki kadarorin.

A wasu kauyukan za a iya barin mace ta noma a filayen da mijin nata ya rasu ya bari, amma ba wai za a bari ta gaje su ba.

Sai dai an fara samun sauyi, saboda nuna goyon baya ga kokarin kwato hakkokin mata, da yawan fadakarwa da kungiyoyin mata ke yi.

Domin a yanzu idan mahaifin mace na da kadarori a birni, to tana da 'yancin da ta gaje su, amma har yanzu ba a barin mace ta gaji kadarorin mahaifinta da ke kauyensu na asali.

Bincike

Binciken da BBC ta yi ya nuna cewa, a yanzu babu wata doka da ta shafi kare hakkin mata ta fuskar gado a duk yankin al'ummar Ibo.

Kome yakan danganta ne ga shawarar da daidaikun iyalai suka yanke, a kan abin da ya kamata mace ta samu a rabon gado, walau a matsayinta na wadda mijinta ya rasu ko kuma marainiya.

Duk da kalubalen da matan kudu maso gabashin Najeriyar ke fuskanta, suna cike da kyakkyawan fatan cewa wata rana za su kai ga matakin da za a rika yin adalci wajen rabon gado.