"Fursunoni na mutuwa a hannun sojin Najeriya"

Jami'an Sojojin Najeriya
Image caption Jami'an Sojojin Najeriya

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International, ta ce daruruwan mutanen da ake tsare da su a Najeriya na mutuwa yayin da sojoji ke fafutikar ganin sun kawad da masu tada kayar baya a kasar.

A wani rahoto da ta fitar, Kungiyar ta danganta mutuwar mutanen ne ga rashin iskar shaka a gidajen kurkuku da kuma bakar yunwar da suke fama da ita tare da kisan da wasu jami'ai ke yi musu.

Rahoton na Amnesty International ya kuma bayyana irin ukubar da mutanen da ake tsare da su ke fuskanta a gidajen kurkuku na sojoji a yankin arewa maso gabashin Najeriyar.

Amnesty ta kara da cewa, saboda yawan mutane da ake kashewa a wuraren da ake tsare da su, har ta kai ga a wasu lokuta a kan binne tarin gawarwaki ne a wuri guda.

Wani jami'in sojin Najeriyar ya shaida wa kungiyar cewa, akalla mutane 950 ne suka mutu a hannun jami'an soji da ke tsare da su tun a farkon wannan shekarar.

Kawo yanzu dai babu wani martani daga rundunar sojin Najeriyar dangane da wannan rahoton, sai dai a baya rundunar sojin ta sha musanta zarge zargen cewa jami'anta na keta hakkin bil'adama.