An hana kiristoci amfani da kalmar Allah

Musulmin Malaysia
Image caption Kiristocin kasar sun ce za su daukaka kara

Wata kotu a Malaysia ta yanke hukuncin cewa Musulmi ne kadai za su iya amfani da Kalmar Allah.

Hukuncin da ya soke wanda wata karamar kotun kasar ta yi a, takaddamar da ta kara zaman dar dar tsakanin mabiya addinai a Malaysian.

Da ta ke amincewa da matakin gwamnatin kasar na aiwatar da wannan ka'ida, kotun ta ce Kalmar ta Allah ba ta zama wani wajibi na addinin kirista ba.

A don haka ba lalle ba ne kiristoci sai sun yi amfani da ita.

A kan hakan kotun ta ce idan har aka bari wadanda ba musulmi ba suna amfani da ita hakan zai kawo rudani a tsakanin jama'a.

Kiristocin sun ce ai suna amfani da kalmar ta Allah ta larabci tun kafin zuwan musulunci.