Gidan abinci mai daukar tagwaye aiki

Wasu tagwaye mata
Image caption Wasu tagwaye mata

Wani gidan abinci dake birnin Moscow na Rasha, ya yanke hukuncin daukar tagwaye, domin jan hankalin masu zuwa cin abinci gurin.

Tagwayen na yin shiga iri daya, domin raba abinci ko abin sha ga wadanda suka je cin abincin dare a gidan abincin.

Mai gidan abincin ya dauki wannan al'ada ce, daga wani tsohon fim na zamanin tarayyar Soviet.

Tagwaye kan zama masu kama da juna, ko kuma kamamminsu ya zama daban, sannan a kan samu tagwaye jinsi daya ko gauraye wato mace da namiji.