Taylor ya fi son zaman kaso a Rwanda

Tohon shugaban Liberia, Charles Taylor
Image caption Mr. Taylor ya yi nuni da matsayin kotun dake cewa yakamata a yi la'akari da iyalan mutum wajen yanke hukuncin inda zai yi zaman jarun

Tsohon shugaban kasar Liberia, Charles Taylor ya nemi a barshi ya yi zaman kurkuku a kasar Rwanda, maimakon Birtaniya.

A wata wasikar da ya aike wa da kotun data yanke masa hukuncin cewa, Mr. Taylor ya ce zai fi sauki da kashe kudi kadan idan yana Afrika ga iyalinsa, idan za su ziyarce shi.

Haka kuma ya bayyana fargabar kai masa hari a kurkukun Birtaniya.

A makon jiya ne wani minista a Birtaniya ya tabbatar da cewa Mr. Taylor zai yi zaman kaso a kasar.