Majalisar dattawan Amurka na dab da cimma matsaya

Shugaban Amurka Barrack Obama
Image caption Shugaban Amurka Barrack Obama

Shugabannin jam'iyyun Democrat da Republican a majalisar dattawan Amurka sun ce suna dab da cimma matsaya da za ta kai ga sake bude harkokin gwamnati da aka rufe da kuma kara yawan kudin da Amurka za ta iya cin bashi.

Jagoran 'yan Democrat a majalisar dattawan, Harry Reid, ya ce tattaunawarsu da 'yan adawa na Republican ta yi armashi sosai.

Ana ganin matsayar za ta bai wa gwamnati damar samun kudaden gudanarwa har zuwa watan Janairu, sannan kuma gwamnatin za ta samu damar kara yawan kudaden da ta ke iya cin bashi har zuwa watan Fabrairu.

Sai dai duk wata matsaya da Majalisar dattawan kasar zata cimma, tilas sai ya samu amincewar 'yan Majalisar wakilan kasar.