Brazil ta sauya hanyar sadarwarta

shugabar kasar Brazil Dilma Roussef
Image caption Brazil ta dau matakin ne saboda zargin satar mata bayanai da Amurka ke yi

Brazil ta ce tana mayar da dukkanin harkokin sadarwarta zuwa wata sabuwar manhajar kwamfuta da hukumar fasahar sadarwar kasar ta kirkiro don hana satar mata bayanai

Ministan sadarwar kasar Paulo Bernardo, ya ce daukar wannan mataki abu ne da ya zama wajibi domin kauce wa satar bayanai.

Ana saran sabuwar manhajar mai suna Expresso V3 za ta fara aikin maye gurbin wadda gwamnatin Brazil din ke amfani da ita ta Microsoft Outlook a cikin wata mai zuwa.

Hukumomin sun ce sabuwar manhajar za ta yi aiki ne da sauran na'urorin sadarwar kwamfuta da ke kasar kawai.

kuma fasalinta zai kare duk wani kokari na satar bayanai daga waje.

Brazil din ta kirkiro wannan manhaja ce sakamakon zargin da aka yi cewa hukumar tsaron Amurka ta na satar bayanan sadarwar gwamnatin kasar.