Nukiliya: Za a tattauna da Iran

Image caption Wakiliyar kungiyar EU da ministan hulda da kasashen wajen Iran

Wakilai daga Amurka da sauran kasashe biyar ma su karfin fadi a ji a duniya za su yi tattaunawa ta kwana biyu da Iran a Geneva kan shirinta na nukiliya.

Tattaunawar ita ce ta farko a hukumance tun bayan Hassan Rouhani ya zama sabon shugaban kasar ta Iran a watan Agusta.

Ministansa na harkokin kasashen waje, Mohammed Javad Zarif ya yi alkawarin gabatar da sabbin shawarwari da za su kai bangarorin kusa da cimma matsaya.

Sai dai jami'an Amurka sun ce ba wanda zai yi tsammanin cimma wata gagarumar nasara a lokaci daya.