Baƙin Haure: An sa dokar ta baci a Sicily

Image caption Dakarun ruwan Italiya masu aikin ceto

An ayyana dokar ta baci a tsibirin Sicily na kasar Italiya, a kokarin taimaka masa tunkarar matsalar daruruwan bakin haure dake isa can ta jiragen ruwa a kowace rana.

Koda cikin sa'a 24 da suka gabata kadai bakin haure 400 ne dakarun ruwan Italiya suka ceto a gabar teku da ta taso daga arewacin afurka zuwa tsibirin Sicily.

Wannan gsgarumin aikin jin kai ga bakin hauren yana cigaba da lashe makuden kudade, kuma yana da sarkakiya sosai, fiye da yadda ya kasance a shekarun baya.

Daruruwan mutane ne dai ke hallaka a teku yayin da suke kokarin tsallakawa Turai daga Afurka da wasu kasashe masu fama da tashin hankali.