Ana ci gaba da takaddama a Amurka

shugaba Obama
Image caption Fadar gwamnatin Amurka ta bukaci majalisar wakilai ta yi koyi da ta dattawa

An ci gaba da samun kiki-kaka a majalisar dattawan Amurka, inda shuwagabanin 'yan jamiyyar Democrat da na Republican ke neman mafuta kan batun bashin kasar.

Amma kuma dukkanin bangarorin sun ce suna dab da cimma matsya a kan yadda za a kara yawan kudaden da Amurka za ta iya cin bashi.

A yau Laraba ne rana ta karshe da muddin ba a cimma matsaya ba a kan batun Amurka za ta rasa kudin da za ta biya basukanta, za a ci gaba da tattaunawar.

Mai Magana da yawun fadar gwamntain Amurka ta White House Jay Carney ya bukaci majalisar wakilai wadda ke neman zama karfen kafa wajen shawo kan matsalar ta yi koyi da ta dattawa.