CAR: Dubban jama'a sun tsere

Image caption Jami'an tsaro na sintiri a Bangui babban birnin kasar

Kungiyar agaji ta likitoci, Medecins Sans Frontieres watau MSF ta ce an tilastawa dubban mutane barin muhallansu a jamhuriyar Afrika ta tsakiya.

A cewarta, tashin hankalin ya kara muni, a don haka kasar na mutakar bukatar agajin gaggawa.

Kasar ta tsunduma cikin rashin tabbas ne bayan da aka hambarar da gwamnatin Francois Bozize a watan Maris.

Kungiyar ta MSF ta ce an kona wasu kyauyuka kurmus.

A makon daya wuce ne Faransa ta ce za ta tura karin dakaru zuwa Jamhuriyar Afrika ta tsakiya don kawo karshen rikicin.

Karin bayani