'Watakila Iran ta bada kai bori ya hau'

Image caption Hassan Rouhani

Iran ta nuna alamun cewa mai yiwa ta baiwa hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai sa ido kan makamashin nukiliya, karin iko na duba makamai.

Hakan a cewar Iran din wani bangare ne na yarjejeniyar da za acinma da za ta kawo karshen ja-in-jar da ake kan shirin nukiliyar kasar.

A rana ta biyu, kuma ta karshe a wannan zagayen tattaunawar tsakanin Iran da manyan kasashen duniya, mataimakin ministan harkokin wajen kasar ta Iran, Abbas Araqchi ya ce watakila muhimmin batun nan na binciken ba-zata , ya kasance cikin matakan karshe da za a cinma yarjejeniya a kansu.

Ya kuma nuna alamun cewa Iran za ta iya amincewa ta rage ayyukan da take gudanarwa na inganta ma'adanin uranium, wanda Amurka ta hakikance cewa za a iya amfani da shi wajen kera makaman nukiliya.

Karin bayani