Amurka ta gamsu da tattaunawa kan nukiliyar Iran

Fadar White House ta Amurka
Image caption Fadar White House ta Amurka

Amurka ta baiyana gamsuwarta ga tattaunawar da aka yi tsakanin Iran da kasashe masu fada a ji na duniya game da shirinta na nukiliya.

Fadar White House ta ce shawarar da Iran ta kawo, ta nuna kyakkyawar niyya da zage dantse da Amurka ba ta taba ganin irinsu daga wajen Iran din a baya ba.

Da take karanta jawabin hadaka na bayan taron a karo na farko a tsakaninsu, wakiliyar tarayyar Turai, Catherine Ashton tace bangarorin biyu sun amince da sake ganawa ranar bakwai ga watan Nuwamba.

Ta kuma ce kafin lokacin masana kimiyya za su tattauna game da matakan da za'a dauka.